Budurwa ta saka saurayinta ya kashe tsohuwar budurwarsa don ya tabbatar da soyayyarsa a gareta

Budurwa ta saka saurayinta ya kashe tsohuwar budurwarsa don ya tabbatar da soyayyarsa a gareta

- A ranar Juma’a 20 ga watan Disamba ne aka yankewa wasu masoya hukuncin shekaru 16 a gidan yari

- An yanke musu hukuncin ne bayan da Sarah Mohammed ta ba wa saurayinta kwarin guiwar kashe tsohuwar budurwarshi

- An ga sakonnin kar ta kwana na Sarah inda take uzzura mishi da ya gaggauta kashe ta su tafi yayin da take jiranshi a kofar gida

A ranar Juma’a 20 ga watan Disamba ne aka yankewa wata daliba mai shekaru 17 hukuncin shekaru 16 a gidan yari. Hukuncin ya biyo bayan karfin guiwar da ta ba saurayinta a kan ya kashe tsohuwar budurwarsa don nuna mata tsananin sonta da yake.

Sarah Mohammed mai shekaru 17, ta tsaya a gaban gidan wacce aka kashe a Openshaw a Manshester na sa’o’I biyu a yayin da take jiran saurayinta, Rhett Carty-Shaw shima mai shekaru 17, don ya kashe mahaifiyar danshi.

A yayin da take jiran saurayin nata, ta tura mishi sakonni sama da 50 don karfafa mishi guiwa da ya yi kisan kan.

Daya daga cikin sakonnin da ta turawa saurayin nata a yayin da take wajen tana jiranshi, shine kamar haka, “Me yasa kake daukan dogon lokaci? Kayi sauri ka aiwatar.”

An yankewa duk su biyun hukuncin zaman gidan yari na shekaru 16 a ranar 20 ga watan Disamba, 2019.

Mohammed ta fara shirya wannan kisan ne tun bayan da ta gano cewa saurayinta na cigaba da dangantaka da tsohuwar budurwarshi mai suna Imam Nasir mai shekaru 17 a duniya.

KU KARANTA: Rikici ya balle a wajen biki, bayan wata budurwa ta zo ta yiwa amarya kwacen miji

Kotun Machester Crown ta saurari wannan shari’ar, an gano cewa Nasir ta tsere wa saurayin nata dakyar ne bayan da yayi mata duka a fuska, wuya da hammata. Ya kuma soketa har sau uku a bayanta.

Carty-Shaw ya bar wajen da ya aikata wannan aika-aikar, inda ya je ya samu budurwarshi dake jiranshi a waje. Sun yi maganganunsu tare da rungume juna sannan suka bar wajen.

Babu dadewa Carty-Shaw ya shiga hannun hukuma bayan da ya sauya kaya tare da gyara wukar don kada a gano abinda yayi.

Bayan an fada bincike, an ga sakonnin sabuwar budurwar tashi inda take ja mishi kunne da kada ya sake ya taba wani abu ta yadda binciken ‘yan sanda zai nuna shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel