Bidiyo: Rikici ya balle a wajen biki, bayan wata budurwa ta zo ta yiwa amarya kwacen miji

Bidiyo: Rikici ya balle a wajen biki, bayan wata budurwa ta zo ta yiwa amarya kwacen miji

- Wani taron biki da aka yi a birnin Mexico ya hargitse sakamakon isowar tsohuwar budurwar ango

- Lamarin ya ba ‘yan biki mamaki don kuwa ta shigo ne a haukace tare da sanar da angon cewa ba zai yuwu yayi aure ba

- Daga nan kuwa ta karasa har gaban amaryar tare da wanke ta da zazzafan mari mai ratsa kumatu

Taron biki ya hargitse ana tsaka da shagalin bikin. Wata mata mai matukar kishi ce ta lalata taron bayan da ta tsallake tarin mutane, don sanar da angon wani mahimmin sako da ya girgiza ‘yan biki.

Anyi wannan karamin ‘wasan kwaikwayon’ ne a birnin Mexico, kamar yadda rahotanni daga can suka nuna.

A bidiyon da aka bayyana, sabbin ma’auratan na shagalin murnar bikinsu ne da kawaye, dangi da abokan arziki kafin matar ta shiga wajen taron. Ta fara ihu da karaji inda ta raba hankulan mutanen da ke wajen.

A yayin da wasu maza majiya karfi suka yi yunkurin hanata isa wajen sabbin ma’auratan, ta yi ihun da kowa ya ji tare da sanar da angon cewa ba zai iya aure ba don tana sonshi.

Cike da ihu take shaidawa angon, “Richard ba zan barka kayi aure ba. Ina sonka, ba zaka yi aure ba,” kafin ta karasa da gudu gaban amaryar inda ta wanke mata fuska da mugun mari.

A lokacin da ta cigaba da ihu da haukarta, anji angon na bada umarnin a fitar da matar.

Ma’abocin amfani da kafar Youtube mai suna Ciro Vazquez, ya bayyana cewa, “Ya kwanta da ita ne kuma ya auri wata.”

Daya daga cikin masu tsokaci ta ce, “Wacce ta auri Richard kuwa ta shiga uku. Ya bayyana cewa bashi da rikon alkawari.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel