Bayan karban tayin Ganduje, da alamun an sake shiryawa Sarki Sanusi wani tarko

Bayan karban tayin Ganduje, da alamun an sake shiryawa Sarki Sanusi wani tarko

Duk da cewa mai martaba sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya amince da matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar Kano, da alamun an sake shirya masa wani sabon tarko. Daily Trust ta bada rahoto.

Wani majiya na kusa da gwamnatin jihar ya bayyanawa Daily Trust cewa duk da cewa ya sarkin ya karbi tayin gwamnan, da sauran rina a kaba.

A cewar majiyar, gwamnatin na kokarin amfani da wasu sharrudan da Sarki ya gindaya a wasikarsa wajen dana masa tarko.

Nan ba dadewa ba, gwamnatin jihar Kano za ta bukaci sarkin Kano ya nemi izinin shugaban karamar hukumar Kano Municipal sabanin al'adar neman izini wajen gwamna kai tsaye.

Bugu da kari, za'a wajabtawa Sarkin Kano budewa sauran sarakunan Gaya, Rano, Karaye da Bichi ofishi a Gidan Makama.

A martanin da Sarkin Kano ya mayarwa gwamna, ya yi tsokaci kan kokarin budewa sauran sarakunan ofishi a Gidan Makama.

A cewar majiyar: "Sarkin ya yi magana da budewa sauran mambobin ofishi. Bari in fada maha, gwamnati za ta bude ofishi ga dukkan sabbin sarakunan da aka nada"

"Bugu da kari, gwamnati za ta bayyana karara cewa duk lokacin da sarki yake bukatan tafiya, ya nemi izinin shugaban karamar hukumarsa."

"Duk lokacin da Sarki ya saba wadannan sharruda, za'a tuhumeshi da rashin da'a kuma za'a iya kwance masa rawani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel