Yanzu-yanzu: DSS ta saki Sowore (Hotuna)

Yanzu-yanzu: DSS ta saki Sowore (Hotuna)

Hukumar tsaro ta farar kaya DSS ta saki jagoran zanga-zangan juyin juya hali ta #RevolutionNow kuma ma wallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

A sakon da shafin Sahara Reporters na Twitter ya wallafa misalin karfe 6:12 na yammacin ranar Talata, 24 ga watan Disamba na nuna Sowore sanye da riga mai launin pink da wanda jeans mai launin bula tare da wani mutum sannan daga baya aka wallafa hotonsa a cikin mota.

Malami ya ce an saki Sowore ne sakamakon belin da wasu kotunna biyu suka ba su.

Magoya bayan Sowore da wani lauya, Mista Abubakar Marshal da ke yi wa Mista Femi Falana aiki ne suka tarbi Sowore.

Ga dai sakon na Twitter a kasa:

A yayin da ya ke barin ofishin na DSS, Dan gwagwarmayar ya mika sakon fatan alheri na bikin Kirsimieti ga 'yan Najeriya tare da cewa babu gudu babu ja da baya kan batun juyin juya hali kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: DSS ta saki Sowore (Hotuna)

Yanzu-yanzu: DSS ta saki Sowore (Hotuna)
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Kano: Sanusi ya haramta wa 'Sokon' Kano shiga fada har abada

Yanzu-yanzu: DSS ta saki Sowore (Hotuna)

Yanzu-yanzu: DSS ta saki Sowore (Hotuna)
Source: Twitter

Yanzu-yanzu: DSS ta saki Sowore (Hotuna)

Yanzu-yanzu: DSS ta saki Sowore (Hotuna)
Source: Facebook

An saki Sowore ne sa'o'i kadan bayan ministan Shari'a kuma Attoney Janar na Taryyar Najeriya, Abubakar Malami ya bayar da umurnin sakinsa tare da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel