Yadda gobara ta lashe matan aure biyu da yara biyar a Katsina

Yadda gobara ta lashe matan aure biyu da yara biyar a Katsina

A lokacin da Shu’aibu Ahmad ya isa Danmusa a jihar Katsina saboda biki, bai taba zaton mummunan hatsarin zai faru ba. Ahmad ya tattara iyalansa ne daga Abuja inda suke zama, don zuwa biki daga nan su zarce hutu a garin.

Bayan kammala bikin, ya tafi ya bar matarsa da yaransa da niyyar su kammala hutunsu sannan daga baya su koma Abuja. Bayan tafiyarsa ne kuwa gobara ta tashi, inda ta lamushe matarsa mai suna Maryam ‘yar shekaru 27 a duniya da ‘ya’yansa.

Ahmad ya bayyana cewa, a ranar Asabar din sun yi waya sama da sau 30 da matarsa inda take tabbatar masa da lafiya suke.

Ya ce: “Na ajiye wayar karshe na cigaba da harkokina. Amma kuma sai hankalina ya kasa natsuwa. A wannan karon da na kirata sai ya ki shiga. Na kira layin kanwarta shima baya shiga. Daga baya sai wani kawuna ya kira da bukatar in hanzarta dawowa gida. Na kira wani kanina, amma yadda naji muryarsa na san ba lafiya ba.”

DUBA WANNAN: Gobara ta tashi a kasuwar wayoyi a Bauchi

Ya kara da cewa, “A nan ne aka sanar dani cewa Maryam ta rasu tare da yaranmu sakamakon gobara da ta lashesu. Ban iya tuki ba, abokina ne ya mayar dani Katsina.”

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta gano, Maryam ta gayyaci wata kawarta gidanta tare da ‘ya’yanta. Bayan sun kammala girke-girkensu ne gobara ta tashi.

Mazauna yankin su bayyana cewa, ba a san silar wannan gobara ba. Sun dai ga wuta ta turnike gidan, amma sunyi kokarin cetosu inda abun ya ci tura. A lokacin da masu ceton suka kai ga dakin, sun tarar dukkansu sun mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel