Kallabi tsakanin rawuna: Ganduje ya nada mace a matsayin shugabar ma'aikatan jiha

Kallabi tsakanin rawuna: Ganduje ya nada mace a matsayin shugabar ma'aikatan jiha

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nada Hajiya Binta Lawan Ahmad a matsayin shugaban ma'aikatan jihar Kano

- Hajiya Binta Lawan Ahmad ta maye gurbin Dakta Kabiru Shehu ne bayan cikar wa'adin aikinsa a makwannin baya

- Hakazalika, Gwamnan ya nada wasu sabbin masu bashi shawara a jihar Kano din

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nadin sabuwar shugabar ma’aikatan jihar, Hajiya Binta Lawan Ahmad.

Kafin a nada ta, Hajiya Binta Lawan Ahmad ita ce babbar sakatariyar ma’aikatar kasuwancin jihar Kano. Hajiya Binta ta maye gurbin Dakta Kabiru Shehu ne, bayan cikar wa’adinsa na aiki a makwannin baya da suka gabata.

Wannan na tattare ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Kano, Abba Anwar ya fitar a jiya Juma’a, ga manema labarai.

DUBA WANNAN: Gobara ta tashi a kasuwar wayoyi a Bauchi

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnan Kano ya amince da nadin masu bashi shawara da suka hada da Ali Baba, a matsayin mai baiwa Gwamnan Kano Shawara a kan harkokin addini, Mustapha Hamza Buhari, a matsayin mai ba gwamnan shawar a kan harkokin siyasa.

Hakazalika, an nada Hamza Usman Darma a matsayin mai baiwa Gwamna shawara a kan abubuwa na musamman, Tijjani Mailafiya Sanka a matsayin mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan harkokin masarautu da kuma Yusuf Aliyu Tumfafi, a matsayin mai baiwa gwamnan shawara a kan harkokin karkara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel