Da idona na kama mijina akan mai aikin mu yana lalata da ita - Matar aure

Da idona na kama mijina akan mai aikin mu yana lalata da ita - Matar aure

- Wata mata mai shekaru 36 mai suna Florence Anyasi ta gurfana gaban kotu da bukatar a tsinke igiyar aurensu

- Ta zargi Stanley da lalata da ‘yar aikinta, yana bibiyar mata tamkar bunsuru, kamar yadda ta ce

- Stanley ya taba saka mata guba a abinci, don yana barazana ga rayuwarta

Wata mata mai shekaru 36 mai suna Florence Anyasi ta shiga tsananin rudani bayan da ta kama mijinta da ‘yar aikinta suna lalata.

Mahaifiyar yara ukun ta tinkari wata kotun kwastamari dake Igando a jihar Legas, da bukatar a tsinke igiyar aurensu mai shekaru 10, bayan da ta kama mijinta kiri-kiri yana lalata da mai aikinta.

Ta kara da bayyanawa kotun cewa, mijinta manemin mata ne. Ta bada labarin yadda take kama mijinta yana bibiyar mata. Mijin nata yana zuwa dakin mai aikinta cikin dare don kwanciya da ita.

“Na kama shi sau ba adadi yana lalata da mai aikina. Wata makwabciyata ta taba tunkarata da bukatar cewa mijina ya kiyayi ‘yar ta. Don yana nemanta da lalata. Na taba kamashi yana tsotsar nonon ‘yar yayata, wacce karamar yarinya ce. Hakazalika, ya saba bibiyar kawayena.” In ji ta.

KU KARANTA: A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma

Fusatacciyar Anyasi ta zargi mijinta Stanley da barazana ga rayuwarta. Ta zargi mijin da sanar da ita cewa zai kasheta kuma ya taba sanya mata guba a cikin abinci.

“Ya siyo min abinci kuma na ci. Bayan na gama ci ne mugun ciwon ciki da amai ya kama ni. An hanzarta kaini asibiti inda aka gano cewa guba ce naci a abinci.” Ta bayyana.

Mai karar ta kara da cewa, mijinta ya mayar da ita tamkar ganga, yana dukanta a kowanne lokaci. Yana kiranta da barauniya kuma karuwa a gaban mutane. Stanley baya bata abinci kuma baya biyan kudin makarantar yara. A don haka take rokon kotu da ta tsinke igiyar aurenta da Stanley.

Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, ya dage sauraron karar zuwa zama na gaba don Stanley ya kare kanshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel