A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma

A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma

- Wata mata ‘yar asalin kasar Rasha ta shiga mummunan hali sakamakon karin girman nono

- Wata kawarta ta zuba mata allurar basilin har kofi 6 cikin nonon don ya kara girma

- Daga baya kuwa sai ya zama ciwo inda nonon ya lalace sai dai likita ya taimaka ya ciresu

Wata mata ‘yar asalin kasar Rasha ta nakasa bayan da aka cire mata nonuwanta. Nonuwan sun lalace ne bayan da tace wata kawarta tayi mata allurar kofi 6 na basilin cikin nonon.

Matar mai shekaru 48 wacce taje neman girman nonon, ta fara samun matsala ne bayan da ta haihu. Ta gano cewa nonon nata ya zube kuma sun kankance.

A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma

A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma
Source: Facebook

Likitar bogin ta nuna mata kyawawan nonuwanta inda tace mata zata iya samun irinsu matukar ta shirya biyan kudin allura na pam 5. Daga nan ne kuwa ta amince da aikin inda ta biya kudin kayan aiki. Kawarta kuwa ta dura mata kofi 6 na basilin cikin kirjinta.

“Gaskiya akwai tsananin azaba, amma inason in yi kyau. Tuni na fara zazzabi kuma na fara dana-sanin abinda nayi. Bayan kwanaki biyu ne azabar ta tafi kuma nonuwana suka zamo abin kallo saboda kyau. Mijina yana ta farin ciki.”

A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma

A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma
Source: Facebook

KU KARANTA: Amfani 12 da aduwa ke yi a jikin dan adam

Daga baya ne fa ciwon nono ya dawo wa matar inda kari mai girma ya tsiro cikin nonuwan.

Ta ce: “Kallonsu kawai abin tsoro ne. Azabar da nake fukanta mai radadi ce. Sun zama ciwo sosai.”

A halin yanzu tana da ta sani kuma tana rokon wasu matan da kada su kuskura su gwada abinda ta yi.

A lookacin da abu yayi tsanani ne suka tunkari asibiti. Tuni kuwa likita yace sai anyi aiki karo na biyu don cire sauran basilin din tare da cire nonuwan baki daya. A lokacin da aka bukaci sanin ko kan nonon zai samu, likitan ya bayyana cewa, ba ta kan nonon yanzu ake ba.ta rayuwarta ake kokarin cetowa.

A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma

A garin neman gira: Hotunan yadda aka cirewa wata mata nonuwa bayan an yi mata ciko domin su kara girma
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel