Buhari ya taya gwamnonin APC da suka samu nasara a kotun koli murna

Buhari ya taya gwamnonin APC da suka samu nasara a kotun koli murna

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya taya gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress APC murnar nasarar da suka samu a kotun kolin Najeriya ranar Alhamis.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu, ya bayyana ne a jawabin da ruwaito Buhari da cewa, "Ina farin ciki da alfaharin cewa kun samu nasara a yakokan kotunku. Lokaci yayi da ya kamata ku fara cika alkawuran da kuka yiwa al'ummarku."

"Wani abun dadi da demokradiyya shine ta kan baiwa kowa daman neman hakkinsa ta kotu..Ina farin ciki kun yi amfani da wannan dama wajen kare kujerunku."

"Tunda komai ya kare yanzu, kada ku huta. Yanzu ya kamata kuyi aiki tukuru domin baiwa al'ummarku shugabanci mai ingancia shekaru hudun da ya rage."

Ina rokon Allah ya kara muku hikima da ingantaccen lafiya wajen aiwatar da ayyukanku."

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar gwamnonin jam'iyar APC takwas a zaben da aka gudanar ranar Laraba, 9 ga watan Disamban 2019.

1. Dapo Abiodun (Ogun)

A jihar Ogun, jam'iyyar Allied Peoples Movement APM da dan takararta, AbdulKabir Akinlade, sun kai gwamnan jihar, Dapo Abiodun, kotu kan rashin amincewa da sakamakon zaben jihar.

A karshe, Kwamitin alkalan kotun kolin karkashin jagorancin Jastis Mary Odili, sun yi ittifakin watsi da kararrakin jam'iyyar APM.

2. Nasir el-Rufai (Kaduna)

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Ashiru ne suka suka shigar da kara gaban kotun domin kalubalantar hukuncin nasarar El-Rufai a zaben gwamnan jihar da INEC ta sanar.

Kwamitin Alkalan bakwai sun yi watsi da karar gaba dayanta.

3. Bello Masari (Katsina)

An tabbatar da Masari matsayin gwamnan jihar, Alkali Inyang Okoro ya yi watsi da karar Yakubu Lado da PDP inda suka bukaci tsige gwamnan kan zargin cewa takardun bogi ya gabatarwa hukumar INEC.

4. Abdullahi Sule (Nasarawa)

Bayan nasarorin da ya samu a kotu zabe da daukaka kara, kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar, Abdullahi Sule, kuma tayi watsi da karar jam'iyyar PDP da David Ombugadu.

5. Babajide Sanwo-Olu (Lagos)

Jam'iyyar Labour Party LP da dantakarta, Ifagbemi Awamaridi da kuma jam'iyyar Alliance for Democracy AD da dan takararta, Owolabi Salis, ne suka shigar da kara kan gwamnan jihar Legas, Jide Sanwoolu.

A karshe, Kwamitin alkalan kotun kolin karkashin jagorancin Jastis Paul Galinje, sun yi ittifakin watsi da kararrakin jam'iyyar AD da LP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Source: Legit

Tags:
Online view pixel