Gamayyar kungiyoyin fafutuka 183 a Kano sun nisanta kansu daga kira ga cire Sarki Sanusi

Gamayyar kungiyoyin fafutuka 183 a Kano sun nisanta kansu daga kira ga cire Sarki Sanusi

Gamayyar kungiyoyin fafuktuka a jihar Kano, da ta kunshi kungiyoyi 183 daban-daban ta nisanta kanta da wasu kungiyoyi 35 da sukayi kira ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya kwancewa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, rawani.

Gamayyar ta yi Allah wadai da dabi'ar wadannan ya tsirari saboda kawai wasu makiyan zaman lafiya da jihar Kano suka dauki nauyinsu.

A wasikar da suka aikawa gwamnan da jami'an tsaro ranar Juma'a dauke da sa hannun shugaban gamayyar, Ibrahim Waiya, da Kakakin gamayyar, MK Adam Rano, sun bayyana cewa basu san da wadanda ke bukatar tsige sarkin Kano ba.

Saboda haka, sun yi kira ga hukumar tsaron farin hula DSS su binciko Ibrahim Ali wanda ya sa hannu kan wasikar kungiyoyin 35.

A jiya Alhamis, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Alhamis ya bayyana cewa ya samu wasika daga kungiyoyin fafufutuka 35 inda suka bukaci ya kwancewa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, rawani kan rashin biyayya.

Mai magana da yawun Ganduje, Abba Anwar, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki inda ya bayyana cewa kungiyoyin sun nuna damuwarsu kan yadda sarkin ke kokarin kafa wata jihar cikin jihar Kano.

Abba Anwar bai lissafa sunayen kungiyoyin ba amma ya ce shugabansu Ibrahim Ali, ya rattafa hannu kan wasikar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel