Ganduje ya nada mace mukamin shugabar kafatanin ma’aikatan jahar Kano

Ganduje ya nada mace mukamin shugabar kafatanin ma’aikatan jahar Kano

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Hajiya Binta Lawan-Ahmed mukamin sabuwar shugabar kafatanin ma’aikatan jahar Kano, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban sakataren watsa labaru na fadar gwamnatin Kano, Abba Anwar ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 20 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Jami’an kwastam sun kai samame kasuwar Mubi, sun tattara buhunan shinkafar waje

Kafin samun wannan cigaba, Hajya Binta ce babbar sakatariyar ma’aikatar cinikayya, kuma ta maye gurbin Dakta Kabiru Shehu ne, wanda ya rike mukamin shugaban ma’aikatan jahar a matakin riko, kuma a cikin makon nan shekarunsa na aiki suka cika, don haka ya yi murabus.

A jawabinsa, Gwamna Ganduje ya bayyana gamsuwarsa da aikin da Kabiru Shehu ya yi a matsayinsa na tsohon shugaban ma’aikatan jahar, inda yace mutum ne mai kishin jahar Kano, wanda kuma ya bauta ma ma’aikatan jahar. “Muna masa fatan alheri.” Inji Ganduje.

Haka zalika gwamnan ya bayyana sabuwar shugabar ma’aikatar a matsayin jajirtacciyar ma’aikaciyar gwamnati wanda ta tsince ayarta a aikin gwamnati, tare da tabbatar da manufarta na ganin ta kawo cigaba a tsarin aikin gwamnati.

Sauran nade naden da gwamnan ya yi sun hada da Ali Baba; mashawarcin gwamnan a kan addinai, Mustapha Hamza Buhari, mashawarcin gwamnan a kan siyasa, Hamza Usman Darma, hadimin gwamnan a kan ayyuka na musamman.

Sauran sun hada da: Tijjani Mailafiya Sanka, mashawarcin gwamnan a kan cibiyar masarautun gargajiyan jahar Kano da kuma Yusuf Aliyu Tumfafi a matsayin mai baiwa gwamnan shawara a kan jama’a. “Ina fata za ku yi aiki tukuru don tabbatar da kun daga likafar jahar Kano zuwa mataki na gaba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel