An cafke gwamnan CBN na bogi (Hotuna)

An cafke gwamnan CBN na bogi (Hotuna)

- Wani dan damfara yanar gizo mai suna Onyebuchi Nwalozie Julius ya shiga hannun EFCC

- Kamar yadda Onyebuchi ya bayyana, yana basaja ne a matsayin Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele

- Ya sanar da hukumar cewa, ya kware wajen lalubo adireshin yanar gizo na mutane don tura musu sakon yaudara

Wani dan damfarar yanar gizo mai suna Onyebuchi Nwalozie Julius, yana garkame a wajen hukumar yaki da rashawa ta EFCC a Uyo, jihar Akwa Ibom. Ana zarginsa ne da sojan gona a matsayin Gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Godwin Emefiele.

Onyebuchi dan asalin Ngor-Okpala ne a jihar Imo, wanda yace yana sana'ar dillanci, ya bayyana cewa yana basaja a matsayin Gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Godwin Emefiele don damfarar mutane.

An cafke gwamnan CBN na bogi (Hotuna)

An cafke gwamnan CBN na bogi (Hotuna)
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya karba nadin da Ganduje yayi masa

Kamar yadda hukumar yaki da rashawan ta bayyana, Onyebuchi ya ce ya damfari wan Omar Es Sh Deeb, wani balarabe. Ya kuma biya kudin ne ta Western Union.

Ya bayyana cewa, ya kware wajen nemo adireshin yanar na mutane da tura musu sakonnin yaudara don samun damfararsu.

Kamar yadda EFCC ta bayyana, duk da Onyebuchi ya amsa cewa ya samu a kalla N4.5m daga damfarar yanar gizon, akwai yuwuwar gano fiye da hakan. Don kuwa ana cigaba da binciko al'amuran damfarar da ya aikata.

An cafke gwamnan CBN na bogi (Hotuna)

An cafke gwamnan CBN na bogi (Hotuna)
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel