Buhari ya nada Farfesa Shashe a matsayin shugaban Asibitin Aminu Kano

Buhari ya nada Farfesa Shashe a matsayin shugaban Asibitin Aminu Kano

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Abba Sheshe a matsayin sabon shugaban likitocin asibitin koyarwa ta Aminu Kano, AKTH a jihar Kano.

Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire ne ya fitar da sanarwar cikin wata takarda mai dauke da sa hannun, Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Enefaa Bob-Manuel a birnin tarayya Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa ministan da kansa ne ya mika wa Sheshe takardan nadin a Abuja.

A yayin da ya ke taya shi murna game da naɗin, Sheshe ya tunatar da shi babban nauyin da ya rataya a kanshi tare da shi na inganta lafiya.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya karba nadin da Ganduje yayi masa

Ministan ya bukaci Mista Sheshe ya tabbatar asibitin Aminu Kano ya cigaba da kasancewa wuri da ke maraba da al'umma.

Ya bukaci sabon CMD ɗin ya dora daga inda wanda ya gada ya tsaya har ta kai ga kasashen ketare za su fara bawa asibitin tallafi da hadin gwiwa.

A cewar sanarwar naɗin da aka yi masa na shekaru hudu ne kuma ya fara aiki ne a ranar 6 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel