Tambuwal zai ginawa Hakiman jiharsa gidaje

Tambuwal zai ginawa Hakiman jiharsa gidaje

Yayinda wasu ke bukatan a kwancewa sarkin gargajiyansu rawani, gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ta kaddamar shirin ginawa hakimai a jihar gidaje.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Aminu Abdullahi Abubakar, mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Mannir Muhammad Dan'iya, ya saki.

Mataimakin gwamnan wanda shi ke jagorantan ma'aikatar kananan hukumomi ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugabannin rikon kwaryan kananan hukumomi 23 na jihar.

Hon Mannir Muhammad ya bayyana cewa wasu daga cikin hakiman basu da gidajen gudanar da ayyukansu saboda haka ya kamata a duba lamarinsu.

Bugu da kari ya bukaci shugabannin rikon kwaryan su kaddamar sunayen makarantun firamaren kananan hukumominsu dake bukatar gyara da tallafi.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel