Sata ta saci sata: Masu garkuwa da mutane sun kashe jagoransu bayan ya tsere da naira miliyan 5

Sata ta saci sata: Masu garkuwa da mutane sun kashe jagoransu bayan ya tsere da naira miliyan 5

Masu iya magana na cewa “Sata gidan barawo rance ne” kuma dama ai zuru bata cin zuru, sai dai a taru a yi zuru zuru, a nan ma wasu gungun miyagu yan bindiga guda ne suka kashe jagoransu bayan sun kama shi satar kudin da suka sato dumu dumu.

Jaridar Information Nigeria ta ruwaito yan bindigan da aka bayyana sunayensu kamar haka; Iweh Kevwe da Emmanuel Ogibi sun kama jagoransu Raymond Enahon ne inda suka daure shi tamau, suka jefar da shi a cikin dajin Obiaruku a jahar Delta, har ya mutu.

KU KARANTA: Kotu ta kwace cibiyar tunawa da Shehu Musa Yar’adua, ta mika ma gwamnatin tarayya

Yansanda na musamman dake karkashin umarnin babban sufetan Yansandan Najeriya, IRT, ne suka samu nasarar cafke miyagun yayin da suke farautar shugaban yan bindigan, Raymond, wanda yayi kaurin suna wajen satar mutane a jahar.

Daga cikin mutanen da suka yi garkuwa dasu akwai tsohon jami’in kudi na jami’ar jahar Delta, wanda basu sake shi ba har sai da iyalansa suka biyasu kudin fansa naira miliyan 5.

Su dai wadannan miyagu suna aiki a matsayin masu gadi a gidaje da kamfanoni ne da rana, amma da zarar dare ya raba sais u dunguma su fita sana’arsu ta satar mutane tare da garkuwa dasu.

A wannan karo dubunsu ta cika ne bayan shugabansu Raymond ya kwashe naira miliyan 5 din da aka biyasu kudin fansa, inda ya tsere dasu ya sayi dalleliyar mota kirar Lexus 330, sai dai sun yi masa dabara a kan cewa zasu yi wata satar da zasu samu naira miliyan 100.

Isarsa keda wuya zuwa mahadarsu suka kama shi, sa’annan suka yi amfani katin cire kudinsa, ATM, suka kwashe duka kudin dake asusunsa. Bugu da kari abokan nasa sun yi awon gaba da motar daya saya, wanda daga bisani suka sayar da ita a kan kudi naira miliyan 1.4.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel