Kotu ta ci tarar jami'an tsaron da suka cafke karuwai a Abuja

Kotu ta ci tarar jami'an tsaron da suka cafke karuwai a Abuja

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, karkashin mai Shari'a Binta Nyako, ta bayyana cewa jami'an tsaro sun yi babban laifi da suka je har cikin gidajen wasu mata masu zaman kansu a garuruwan dake wajen Abuja kuma suka kama su.

Jastis Binta Nyako ta ce, ba karamin laifi bane da jami'an suka take hakkin matan har cikin gidajensu suka kama su. Hakan ta faru ne a watan Fabrairu na 2017, saboda sun zargi matan da karuwanci.

Jami'an tsaro na tafi da gidanka na hukumar tsaftace Abuja tare da hadin guiwar 'yan sanda da sojoji ne suka yi kamen karuwan a wancan lokacin.

Wannan hukuncin da kotu ta zartar ya biyo bayan ruwa da tsaki da wata kungiyar lauyoyi tayi wajen kare hakkin matan da aka cafke din.

Wata mata mai suna Constance Nkwocha ce tare da wasu mata 15 ne suka shigar da karar.

Sun maka 'yan sanda, sojoji da kuma ministan babban birnin tarayyar a gaban kuliya.

DUBA WANNAN: Tirkashi: Ku raba ni da ita, ta yi zina da maza har tara - Miji mai neman saki

"Shiga har cikin gida da aka yi aka kamo wadannan matan, take musu hakki ne. Kuma shiga gonarsu ce. Saboda doka ta basu damar kadaicewa a cikin gidajensu, ba tare da wani ya kutsa musu ba." In ji mai shari'a Binta Nyako.

"Ita dai doka ba kara zube take ba. Saboda haka akwai shimfidaddun ka'idojin da za a bi kafin a kama mutum. Don haka ya zama wajibin jami'an tsaron da su rika taka tsantsan. Su bi yadda doka ta gindaya." cewar mai shari'ar.

Dag nan ne kotu ta umarci wadanda aka kai karar da su biya kowacce mace mai zaman kanta N100,000.

Lauya mai shigar da kara ya shaida wa kotu cewa jami’an tsaron da suka je kamen sun yi wa karuwan satar kudaden su a gidajen da suka kamo su.

Kungiyar kare hakkin matan ta ce bayan an kama su, an kwashe musu kudade sannan kuma an gallaza musu azaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel