Kotu ta baiwa EFCC izinin cigaba da tsare Adoke domin gudanar da bincike

Kotu ta baiwa EFCC izinin cigaba da tsare Adoke domin gudanar da bincike

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta samu daman cigaba da tsare tsohon ministan sharia a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Mohammad Bello Adoke.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wata babbar kotun Abuja ce ta baiwa EFCC wannan izinin na tsare Bello Adoke tsawon kwanaki 14 domin gudanar da cikakken bincike a kansa biyo bayan zarginsa da take yi da hannu cikin aikata laifin rashawa.

KU KARANTA: Kotu ta kwace cibiyar tunawa da Shehu Musa Yar’adua, ta mika ma gwamnatin tarayya

A ranar Alhamis ne jami’an Yansandan kasa da kasa watau INTERPOL ta taso keyar Adoke zuwa gida Najeriya bayan kama shi da ta yi a kasar Dubai tsawon makonni 5 da suka gabata, INTERPOL ta kama shi bisa umarnin kasar Dubai, bayan gwamnatin Najeriya da Dubai sun tattauna batun.

EFCC na tuhumar Adoke ne da zargin hannu cikin badakalar sayar da rijiyar hakan danyen main a OPL 245 ga kamfanonin Shell da ENI, don haka Alkalin kotun, mai sharia Othman Musa ya bayar da wannan umarni ga EFCC domin ta gudanar da bincike yadda ya kamata.

A wani labarin kuma, shugaban hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana cewa sun gurfanar da fiye dalibai 100 masu satar amsa gaban kotu, kuma 20 sun samu hukuncin dauri a gidan maza.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Oloyede ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da masu cibiyoyin zana jarabawar JAMB da ake amfani da na’urar kwamfuta, a garin Kaduna inda yace suna cigaba da tuhumar sauran dalibai barayin amsa guda 80 a kotuna daban daban.

JAMB ta shirya wannan taro ne domin fara wayar da kan masu cibiyoyin jarabawar game da shirye shiryen da take yi ma jarabawar JAMB na shekara 2020, inda ya gargadesu da cewa hukumar ba za ta sassauta a kan laifin satar amsa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel