Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya karba nadin da Ganduje yayi masa

Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya karba nadin da Ganduje yayi masa

A yau ne Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ya amince da nadin da Gwamna Abdulahi Umar Ganduje yayi masa na shugabantar majalisar sarakunan jihar.

Idan zamu tuna, a ranar 9 ga watan Disamba ne Ganduje ya nada Sanusi a matsayin shugaban majalisar sarakuna jihar kuma ya umarcesa da "ya gaggauta kiran taron rantsarwa na sauran 'yan majalisar kamar yadda doka ta tanadar."

Amma kuma, bayan makonni da zabar Sarki Sanusi, an zargesa da barin gwamnan a cikin duhu na ya karba ko bai karba ba. Lamarin da yasa gwamnan ya bashi wa'adin kwanaki biyu a kan sanar da matsayarsa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamnoni sun bayyana matsayarsu kan biyan mafi karanci albashi N30,000

A wasikar wa'adin da mika wa Sarkin, gwamnan ya ce, "karbar nadin ko akasin hakan ya samu mai girma Gwamnan jihar Kano a cikin kwanaki biyu da aka samu wasikar nan."

Amma kuma, ko sa'o'i 24 ba a yi ba da bada wa'adin, sarkin ya karba wannan nadin a wasika mai kwanan wata 19 ga watan Disamba wacce sakataren masarautar, Abba Yusuf yasa hannu.

A wasikar da jaridar Daily Nigerian ta gani, sarkin ya bayyana cewa bai yi watsi da wannan nadin ba. Sarki Sanusi ya kara da bukatar umarnin Gwamna Ganduje a kan nadin sauran 'yan majalisar

Kamar yaddda sarkin ya ce, akwai bukatar Ganduje ya bada wani umarni a kan nada sauran 'yan majalisar kamar yadda tanadin dokar ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel