Ya zama wajibi mu kara farashin wutan lantarki - Ministan Lantarki

Ya zama wajibi mu kara farashin wutan lantarki - Ministan Lantarki

Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin kara farashin wutan lantarki yayinda take shirin kammala wasu ayyuka a fadin tarayya, ministan lantarki, Injiniya Saleh Mamman, ya laburta.

Ya ce kara farashin ya zama wajibi saboda tsadar samar da wutan lantarki a kasar, kuma hakan na shafan kamfanonin wuta a kasar.

A yanzu haka, an baiwa kamfanonin raba wutan daban-daban daman sanya farashin wuta da kuma tabbatar da cewa kwastamomi na biyan kudi ne bisa ga wutan da sukayi amfani da shi.

Minista Saleh Mamman yace: "A cikin kokarin da akeyi na inganta wutan lantarki a Arewacin Najeriya, gwamnati za ta samar da sabon 330KVA."

Wannan na cikin ayyukan da mukeyi domin inganta wutan lantarki a Najeriya. Idan aka samu ingancin wuta, ya zama wajibi mu kara farashin wuta, saboda wajibi ne masu samar da wutan su samu kudin aikinsu."

DUBA NAN: Buhari ya yaye daliban kwalejin yan sanda 628 a Kano (Hotuna)

Ya yi kira ga Najeriya su kasance masu tsoron Allah ta hanyar biyan kudin wuta kuma ya bada tabbacin cewa gwamnatin na iyakan kokarinta wajen kammala ayyukan da ke tafiye domin inganta wutan lantarki.

A zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, gwamnati ta sayar kayayyakin samar da wutan lantarki ga wasu masu hannun jari domin gani ko zasu iya kawo sauyi.

Amma bayan shekaru da sayar musu, har yanzu babu wani ingantaccen sauyi da aka samu. A yanzu gwamnati na shirin kwato kamfanonin daga hannunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel