Yanzu-yanzu: Ganduje ya baiwa Sarki Sanusi kwana biyu kacal

Yanzu-yanzu: Ganduje ya baiwa Sarki Sanusi kwana biyu kacal

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya baiwa mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, kwana biyu ya amince da mukamin shugaban majalisar sarakuna ko kuma yayi watsi da shi.

Za ku tuna a ranar 9 ga watan Disamba, 2019, gwamnan ya nada Sarkin Kano matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar amma har yanzu Sarkin bai furta uffin kan tayin ba.

A wani wasika da aka aikawa fadar sarkin daga ofishin babban sakataren gwamnatin jihar, gwamna Ganduje ya bukaci sarkin yayi martani kan tayin da akayi masa cikin kwanaki biyu da karbar wasikar.

Wasikar na dauke da kwanan wata 19 ga Disamba, 2019.

Sai dai wasu na keke da keke da Sarki Sanusi sun ce har yanzu Sarki bai yi ido biyu da takardar nadin ba ballantana ya mayar amincewa ko watsi da mukamin shugaban majalisar sarakuna ba.

Yanzu-yanzu: Ganduje ya baiwa Sarki Sanusi kwana biyu kacal

Yanzu-yanzu: Ganduje ya baiwa Sarki Sanusi kwana biyu kacal
Source: Facebook

A bangare guda, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Alhamis ya bayyana cewa ya samu wasika daga kungiyoyin fafufutuka 35 inda suka bukaci ya kwancewa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, rawani kan rashin biyayya.

Mai magana da yawun Ganduje, Abba Anwar, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki inda ya bayyana cewa kungiyoyin sun nuna damuwarsu kan yadda sarkin ke kokarin kafa wata jihar cikin jihar Kano.

Abba Anwar bai lissafa sunayen kungiyoyin ba amma ya ce shugabansu Ibrahim Ali, ya rattafa hannu kan wasikar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel