Rahama Sadau: Yadda za'a kawo gyara a harkar fina-finan Hausa

Rahama Sadau: Yadda za'a kawo gyara a harkar fina-finan Hausa

- Jaruma Rahama Sadau ta bayyana cewa, babu wani cigaba da masana’antar Kannywood ta samu a 2019

- Ta bayyana cewa, yanzu harkar fim din duk ta faduwa ce tunda ba a buga sidi. Sinima kadai ake samun kudi

- Jarumar ta roki gwamnati da ta gina Sinimu a kalla guda biyar a garuruwan Arewa don a samu habaka a harkar

Fitacciyar jarumar masana’antar fina-finai, ta bayyana cewa babu wani ci gaba da masana’antar fim ta samu a wannan shekarar ta 2019 me shudewa. Ta yi gargadin cewa, idan har ba a dauki babban mataki ba, to ba za a samu ci gaba a harkar ba.

Rahama tayi wannan kalami ne a wata hira ta musamman da tayi da mujallar Fim.

Jarumar kuma Furodusar fim din ‘Rariya’, ta ce, “Gaskiya babu maganar cigaba a masana’antar fim a wannan lokacin da muke ciki. Saboda idan ka duba gaba daya, idan furodusa yayi fim a wurin yake iya saida fim din – siniman Kano.

“Muna da jihohi 19 a Arewa, kuma duk suna kallon fim. A wani lissafi da aka yi, an fi kallon fina-finan Hausa a kan na Kudu. Amma wannan kasuwar ta lalace, sinimar kawai ake iya kallon fim.

“Yanzu, sai dai ka yi fim kawai dan Kano ya kalla. Don haka ka gaya mani ta inda cigaba yake. Wanda a da kai ka san idan ka yi fim ka buga sidi da fim daya, sai ka yi kudi. Banda yanzu, saboda kowa ja baya yake yi. Babu wanda zai zuba kudinshi yayi fim, kudin su ki fitowa.

KU KARANTA: Yadda kaza guda 1 ta zama sanadiyyar arzikin wani matashi, inda ta kawo masa shanaye 150

Da mujallar fim ta tambaye ta shawarar da zata bada don shawo kan wannan matsalar, sai jarumar ta ce: “Kullum idan muka zauna muna magana, na kan ce kamata yayi a samar da sinimu ko guda biyar ne a garuruwan da aka san cewa sun fi kallon fina-finan hausa.”

Jarumar ta roki gwamnati da ta tallafa ta gina sinimu a garuruwan Arewa. Ta bayyana cewa, suna biyan haraji kuma a shirye suke da su cigaba da biyan harajin. Hakan ne kadai zai zama mafita garesu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel