Makarantu ya kamata ka gina ba Masallatai 95 ba - Martanin 'yan Najeriya ga gwamnan jihar Jigawa

Makarantu ya kamata ka gina ba Masallatai 95 ba - Martanin 'yan Najeriya ga gwamnan jihar Jigawa

- Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana cewa zata gina masallatai 95 a fadin jihar

- Lamarin ya jawo cece-kuce, ganin cewa jihar na daya daga cikin jihohi koma baya a bangaren ilimi

- Masu tsokaci tare da kushe wannan yunkurin, sun ce da gwamnan zai duba gina masana’antu da makarantu, da hakan yafi

Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana cewa zata gina masallatai 95 a fadin jihar. Wannan lamarin kuwa ya jawo cece-kuce daga ma’abota amfani da kafar sada zumuntar zamani ta tuwita. Sun bayyana cewa, jihar na da sama da yara 800,000 da basu zuwa makaranta, amma gwamnatin na shirye-shiryen fara gina masallatai.

Wasu daga cikin masu tsokacin, sun bukaci sanin ta yadda sabbin masallatan zasu habaka jama’ar jihar ko samar musu da aiyukan yi. Wasu daga ciki sun shawarci gwamnan jihar da ya duba gina masana’antu ko makarantu a maimakon massallatan.

Masu tsokacin sun bayyana cewa, ba wai saboda masallatai bane za a gina suke guna-guni, ko majami’u 95 gwamnan yace zai gina sai sun sokeshi.

KU KARANTA: Amfanin ganyen dalbejiya guda 16 a jikin dan adam

Jihar na da manyan bukatu a bangarori da dama na cigaba. Akwai masallatai da mutane nagari masu kishin addini suke ginawa. A don haka ne ba sai gwamnati ta saka hannu wajen kara gina wasu ba.

Hakkokin jama’ar jihar da suka rataya a wuyan gwamnati sun hada da ilimi, habaka tattalin arzikin jihar, samarwa matasa aikin yi, inganta makarantu, habaka fannin lafiya da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel