Tsoffin gwamnoni 22 ake bincika a kan rashawa - Malami

Tsoffin gwamnoni 22 ake bincika a kan rashawa - Malami

Ministan shari'a, Abubakar Malami ya ce gwamnoni 22 ne ake bincika a kan rashawa. Gwamnan ya sanar da hakan ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, yayin da yake zantawa da manema labarai.

Yayin tattaunawa da manema labarai, Abubakar Malami ya bayyana cewa tsoffin gwamnoni uku ne aka yankewa hukunci a kan rashawa, a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsoffin gwamnonin da aka yankewa hukunci a kan rashawa sun hada da Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato, tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame da kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.

Ya ce, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yankewa mutane 1,636 hukunci a kan laifukan da suka danganci rashawa tun daga 2015 zuwa watan Satumba na 2019.

"Abin farin ciki ne ka gane cewa, hatta tsoffin gwamnoni ko sanatoci masu ci yanzu ba a kyale ba," Malami ya ce.

DUBA WANNAN: Ganduje: Sabbin dokokin masarautu za su fara aiki

"A halin yanzu, akwai manyan mutane da suka hada da ma'aikatan fannin shari'a da tsoffin gwamnoni da aka kama da laifin rashawa, kuma an gurfanar dasu tare da yanke musu hukuncin zaman gidan gyaran hali," ya kara da cewa.

"Akwai tsoffin gwamnoni uku da aka yankewa hukunci, wadanda a halin yanzu suke garkame a kan rashawa da sauran laifuka madangantansu. A halin yanzu kuma akwai tsoffin gwamnoni 22 da ke gaban kuliya kuma ana bincike a kansu." cewar ministan.

Ministan ya ce, kungiyoyin yaki da rashawa basu duba wata sanayya ko son kai kuma basu da nufi a kan kowanne mutum ko kuma kungiya.

"Yaki da rashawa ana yinsa ne baki daya, a kammale amma ba tare da an hari wata jam'iyyar siyasa ba ko kabila," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel