Zamfara: Matawalle ya kwace kwangilar N76bn

Zamfara: Matawalle ya kwace kwangilar N76bn

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya janye kwangilar N79.6bn da aka ba kamfanoni daban-daban da suka hada da Alliance Trading Company, wanda mallakin Adamu Aliero ne, tsohon gwamnan jihar Kebbi.

Kwangilar da ta kai darajar N25bn da aka ba Alliance Tradin Company Limited da wata mai darajar N27bn da aka ba China Zhonghao a 2013 da 2018, duk Gwamna Matawalle ya kwacesu a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba, 2019.

Kwamishinan aiyukan jihar, Ibrahim Isa Mayana ya tabbatar da wannan cigaban kuma ya sanarwa manema labarai. Ya ce an bukaci 'yan kwangilar dasu dawo da kudaden ko su fuskanci fushin hukuma.

DUBA WANNAN: Marin dan majalisa: Majalisar jihar ta bukaci a cafko shugaban karamar hukuma

Ya kara da bayyana cewa, wasu daga cikin kwangilar da aka kwace ba a yi su yadda ya dace ba ko kuma an barsu ba tare da kammalawa bane, duk da 'yan kwangilar sun amshe makuden kudaden.

Mayana ya ce:"An ba China Zhonghao kwangilar haka famfon burtsatse 84 a wasu karkara a kan N27.694bn a 2018, kuma na biyasu N14.477. Amma sun bar kwanagilar bayan da suka kammala kashi 13 daga cikinta."

"An ba kamfanin Alliance trading kwangilar N25.992bn don zagaye wasu yankunan karkara na kananan hukumomi 14 da wutar lantarki a 2013. A biya N22.599bn amma kamfanin ya bar kwangilar bayan da ya kammala kashi 67 a ciki." cewar Mayana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel