Kotu ta kwace cibiyar tunawa da Shehu Musa Yar’adua, ta mika ma gwamnatin tarayya

Kotu ta kwace cibiyar tunawa da Shehu Musa Yar’adua, ta mika ma gwamnatin tarayya

Wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja dake zamanta a unguwar Maitama a karkashin jagorancin Alkali mai sharia Baba H Yusuf ta yanke hukuncin kwace cibiyar tunawa da marigayi Shehu Musa Yar’adua.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito hukumar yaki da rashawa ta ICPC ce ta gabatar da bukatar haka ga kotun biyo bayan tuhumar cibiyar da take yi da kin biyan kudaden haraji, kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Rasheedat Okoduwa ta bayyana.

KU KARANTA: Kaico! Kasa ta danne kananan yara 3 da ransu a garin Kaduna, sun sheka barzahu

Kaakakin hukumar ta ce ICPC ta nemi kotun ta bata ikon karbe cibiyar Shehu Musa Yar’adua ne tare da wasu manyan kadarori guda 24 dake cikin garin babban birnin tarayya Abuja ne saboda rashin biyan kudaden haraji da a jimlace ya kai naira biliyan 8.6.

Sai dai kaakakin ta kara da cewa a maimakon kamfanonin su biya wadannan bashin kudaden haraji da ake binsu, sai suka musanta mallakar kadarorin, “Don haka sai aka aika ma mataimakin shugaban kasa takardar korafi, wanda shi kuma ya aika ma ICPC domin ta dauki matakin daya kamata.”

Sai dai a yayin da ake sharia’ar, kamfanoni guda uku; Frankdiowo Nigeria Limited, Kati Nigeria Limited da R.Timmermann & Co Nigeria Limited sun bayyana gaban kotu, kuma sun gabatar da dalilansu da suke ganin bai kamata a kwace musu kadarori ba.

Sai dai bayanan kamfanin Frankdiowo ne kadai suka gamsar da kotu, kuma ta sallamesu, amma sauran kamfanoni guda biyu zasu cigaba da bayyana gaban kotu domin a cigaba da gudanar da shari’ar.

Daga karshe Rasheedat ta ce yawancen kadarorin da kotu ta mika mallakinsu ga ICPC suna manyan unguwannin cikin babban birnin tarayya Abuja ne, da suka hada da Wuye, Jahi, Utako, Wuse, Garki II da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel