Dakarun Sojin sama sun yi watsa watsa da matattarar mayakan Boko Haram a Borno

Dakarun Sojin sama sun yi watsa watsa da matattarar mayakan Boko Haram a Borno

Rundunar mayakan sojan sama ta Najeriya ta sanar da tarwatsa wasu sansanonin da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram take jibge makamanta da motocin hawanta dake yankin Arewacin jahar Borno.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya NAN, ta ruwaito daraktan watsa labaru na rundunar Sojan saman, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 19 ga watan Disamba inda yace rundunar ta yi amfani da jirage yakinta ne wajen kai wannan hari.

KU KARANTA: Kaico! Kasa ta danne kananan yara 3 da ransu a garin Kaduna, sun sheka barzahu

Daramola yace dakarun rundunar sun kaddamar da wannan hari ne a yankin Bakare, wani karamin tsibiri dake cikin tafkin Chadi, inda jiragen yakin rundunar Sojan suka kai wasu hare hare a matattarar makamai da motocin yan ta’addan.

“Mun hangi ma’ajiyan makaman suna ta ci da wuta a sakamakon bamabaman da jiragenmu suka saukar a kan su, wannan aiki na harbin maciji an kirkireshi ne domin tarwatsa wasu sanannu kuma zababbun ma’ajiyar Boko Haram tare da sansanoninsu.

“Yana daya daga cikin sassan ayyukan Soji da muke yi tare da Sojojin kasa domin gamawa da kakkabin yan Boko Haram da suka rage, tare da kawo karshen ayyukan yan ta’adda a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Al’ummar garin Ngugo na karamar hukumar Ikeduru na jahar Imo sun shiga halin firgici da damuwa biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kaddamar a kan wani mutumi da dansa, inda suka kashesu har lahira.

Yan bindigan sun kashe mista Frank Nzeji da dansa Lawarence Obinna wanda bai dade da dawowa Najeriya daga kasar Amurka ba, ne yayin da suka kai ziyara gidan wani abokin mahaifinsu a garin Ogoni na jahar Ribas.

Yan bindigan dake sanye da kayan Sojoji sun bude ma mutanen wuta ne a cikin gidan da suka je bakunta yayin da suka yi ido hudu dasu, haka zalika shi ma direban daya tukasu a ranar, wanda dan uwansu ne ya samu rauni a dalilin harbin, kuma shi ya sanar da yan uwansu a gida halin da ake ciki, amma daga bisani ya mutu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel