Kotu ta daure dalibai 20 da aka kama suna satar amsa yayin zana jarabawar JAMB

Kotu ta daure dalibai 20 da aka kama suna satar amsa yayin zana jarabawar JAMB

Kiran ruwa ba lema, inji masu iya magana, a nan ma shugaban hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana cewa sun gurfanar da fiye dalibai 100 masu satar amsa gaban kotu, kuma 20 sun samu hukuncin dauri a gidan maza.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Oloyede ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da masu cibiyoyin zana jarabawar JAMB da ake amfani da na’urar kwamfuta, a garin Kaduna inda yace suna cigaba da tuhumar sauran dalibai barayin amsa guda 80 a kotuna daban daban.

KU KARANTA: Kaico! Kasa ta danne kananan yara 3 da ransu a garin Kaduna, sun sheka barzahu

JAMB ta shirya wannan taro ne domin fara wayar da kan masu cibiyoyin jarabawar game da shirye shiryen da take yi ma jarabawar JAMB na shekara 2020, inda ya gargadesu da cewa hukumar ba za ta sassauta a kan laifin satar amsa ba.

“Mun gurfanar da barayin amsa mutum 100 a duk fadin Najeriya, kuma zuwa yanzu mutane 20 sun fuskanci hukuncin dauri, yayin da mu ke cigaba da tuhumar sauran a gaban kotun. Don haka a shekarar da ta gabata mun gurfanar da barayin amsa ne, amma shekara mai zuwa zamu gurfanar da masu cibiyoyin jarabawar ne.” Inji shi.

Don haka Oloyede ya yi kira ga masu cibiyoyin dasu kauce ma gudanar da magudin jarabawa, kuma su tabbata sun bi dokokin da hukumar ta shimfida musu sau da kafa domin kauce ma gurfana gaban kotu.

Shugaban na JAMB yace zuwa yansu akwai cibiyoyin jarabawar JAMB guda 613, kuma sun cire guda 133, sa’annan suka maye gurbinsu da wasu sabbin 133, haka zalika ya tabbatar ma dalibai cewa babu wanda zai zana jarabawar din 2020 ba tare da ya mallaki lambar katin shaidan dan kasa ba.

Daga karshe ya bayyana cewa sun shiga yarjejeniya da hukumar rajistan dan kasa domin su baiwa dalibai masu bukatar zana jarabawar fifiko wajen yi musu rajistan domin su samu lamar NIN cikin sauki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel