Yanzu-yanzu: Gwamnoni sun bayyana matsayarsu kan biyan mafi karanci albashi N30,000

Yanzu-yanzu: Gwamnoni sun bayyana matsayarsu kan biyan mafi karanci albashi N30,000

Gwamnonin jihohin Najeriya karkashin kungiyar gwamnoni ta NGF, sun sake jadada aniyarsu na amincewa da biyan N30,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma'aikata a jihohinsu.

Shugaban kungiyar, Kayode Fayemi ne ya yi wannan jawabin a babban birnin tarayya Abuja yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a karshen taron kungiyar a Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Fayemi ya ce ba gaskiya bane ikirarin da Hukumar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi na cewa akwai gwamnonin da ba su fara tattaunawa da rassan kungiyar kwadago na jihohinsu ba kan yadda za a aiwatar da tsarin biyan albashin.

DUBA WANNAN: Kano: Bidiyon yadda masu neman aiki ke haura katanga da taga a hukumar NDLEA ya janyo cece-kuce

Fayemi ya ce, "Abinda zan fada muku shine babu jihar da za ta biya albashi kasa na N30,000 idan an mun kai matsayar."

Da ya ke karanto sakon bayan taron na 2019, shugaban kungiyar ya ce kungiyar ta samu rahoto kan taron saka hannun jari tsakin Afrika da UK da za a gudanar a 2020 daga ofishin jakadancin UK karkashin jagorancin babban kwamishin UK a Najeriya, Misis Harriet Thompson.

Fayemi ya ce Farai Ministan Ingila ne zai karbi bakuncin wadanda za su hallarci taron da suka hada da 'yan kasuwa, gwamnatoci, hukumomi na kasa da kasa domin yin baje kollin guraben saka hannun jari da ake da su a Afirka a Janairun 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel