Boko Haram sun kai hari garuruwan Borno 6 cikin makonni uku - Gwamna Zulum

Boko Haram sun kai hari garuruwan Borno 6 cikin makonni uku - Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna bacin ransa kan hare-haren da Boko Haram ke kaiwa kauyuka da garuruwa a karamar hukumar Askira-Uba ta jihar.

Wannan ya biyo bayan harin da Boko Haram suka kai kauyen Chul a makon nan, bayan wanda suka kai Rumirgo, Lassa, Mussa, Kufa da Gwandam a makonni uku da suka gabata.

Mai ba gwamnan shawara kan harkokin sadarwa, Malam Isa Gusau, ya bayyana cewa sabanin tunanin da akeyi na cewa an turke yan ta'addan a tafkin Chadi, har yanzu suna shiga wasu sassan jihar sun aikata ta'asa.

DUBA NAN: Na samu wasika daga kungiyoyin Kano 35 na bukatar sauke Sarkin Kano - Ganduje

Gusau yace: "Gwaman Babagana Umara Zulum na nuna damuwarsa kan hare-haren da Boko Haram suka kai Rumirgo, Lassa, Mussa, Kufa, Gwandam, da Chul a karamar hukumar Askira-Uba ta jihar."

"Gwamnan na jajintawa wadanda hare-haren ya shafa kuma ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa na cigaba da kokarin kawo karshen lamarin tsaron jihar."

"Gwamnan zai kai ziyara karamar hukumar Askira-Uba inda ya je kudancin jihar kwanan nan."

"Gwamnan ya tabbatarwa al'ummar cewa gwamnati zata taimaka musu. Bugu da kari, gwamnatin za ta cigaba da baiwa jami'an Soji goyon baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel