Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun cafke wani ministan Jonathan a filin jirgi

Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun cafke wani ministan Jonathan a filin jirgi

- Tsohon ministan shari’a, Mohammed Adoke, ya iso Najeriya a kan idon hukumar EFCC

- An cafke Adoke ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe a ranar Alhamis

- Ana zargin tsohon ministan ne da laifuka da suka hada da amfani da kujerarsa ba ta yadda ya dace ba

Tsohon ministan shari’a, Mohammed Adoke ya dawo kasar Najeriya a kan idon hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Channels TV ta ruwaito cewa, jirgin da Adoke ke ciki ya sauka a filin jirgin da karfe 3:40 na yammacin yau Alhamis, 19 ga watan Disamba.

Legit.ng ta gano cewa, jirgin na sauka jami’an tsaro suka yi awon gaba dashi zuwa ofishin ‘yan sandan kasa da kasa dake birnin tarayya.

Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun cafke wani ministan Jonathan a filin jirgi

Mohammed Adoke a cikin motar EFCC daga filin jirgi
Source: UGC

Ana zargin Adoke da laifin amfani da kujerarsa ba ta yadda ya dace ba da kuma almundahanar wasu makuden kudade.

DUBA WANNAN: Ganduje: Sabbin dokokin masarautu za su fara aiki

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta zargi ministan da wasu laifuka tare da wasu mutane hudu a madadin gwamnatin tarayyar Najeriya.

Kamar yadda rahoton PM News ya bayyana, EFCC ta cafke tsohon ministan shari’ar Najeriyar ne bayan saukarsa daga Dubai.

Jami’an EFCC din na filin jirgin a yayin da ya sauka, kuma sun tabbatar da za a gurfanar dashi a gaban kuliya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel