Miyagu sun halaka Uba da Dansa da ya kawo ziyara daga kasar Amurka a jahar Imo

Miyagu sun halaka Uba da Dansa da ya kawo ziyara daga kasar Amurka a jahar Imo

Al’ummar garin Ngugo na karamar hukumar Ikeduru na jahar Imo sun shiga halin firgici da damuwa biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kaddamar a kan wani mutumi da dansa, inda suka kashesu har lahira.

Jaridar Punch ta ruwaito yan bindigan sun kashe mista Frank Nzeji da dansa Lawarence Obinna wanda bai dade da dawowa Najeriya daga kasar Amurka ba, ne yayin da suka kai ziyara gidan wani abokin mahaifinsu a garin Ogoni na jahar Ribas.

KU KARANTA: Buhari ya bayyana alhininsa game da rashin dan uwansa Abdullahi Dauda

Yan bindigan dake sanye da kayan Sojoji sun bude ma mutanen wuta ne a cikin gidan da suka je bakunta yayin da suka yi ido hudu dasu, haka zalika shi ma direban daya tukasu a ranar, wanda dan uwansu ne ya samu rauni a dalilin harbin, kuma shi ya sanar da yan uwansu a gida halin da ake ciki, amma daga bisani ya mutu.

Wani matashi ne ya yi karfin hali ya kwashe gawarwakin mamatan zuwa wani cibiyar ajiyan gawa dake garin Aba na jahar Abia bayan ya sanar da rundunar Yansandan jahar Ribas halin da ake ciki. Daga bisani kuma aka garzaya da gawarwakin zuwa dakin ajiyan gawa na asibitin kwararru na jahar Imo dake Owerri.

Matar da aka kashe mijinta da danta, Felicia Nzeji ta bayyana cewa danta mazaunin Greenville ne dake jahar South Carolina a kasar Amurka, kuma ya dawo gida ne domin ya yi aure, ta kara da cewa budurwa Obinna ce ta sanar da Yansandan SARS na Imo game da kisan.

Uwargida Feliciz tace daga bisani Yansanda sun kama budurwar tare da kanin Obinna, inda suka musu tambayoyi bayan nan kuma suka sake su, daga karshe an mayar da maganan zuwa sashin binciken laifukan kisan kai na rundunar Yansandan jahar Imo domin gudanar da cikakken bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel