Najeriya na tsumayin shigowar jiragen dankaro 60 makare da kayayyaki, 55 sun iso

Najeriya na tsumayin shigowar jiragen dankaro 60 makare da kayayyaki, 55 sun iso

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA ta sanar da cewar tana tsumayin isowar wasu gingima gingiman jiragen dankaro guda 60 dauke da kayayyaki daban daban zuwa tashoshin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito hukumar NPA ta bayyana haka ne cikin takardar bayanan hukumar da take fitarwa a kullum mai suna ‘Shipping Position’ a ranar Alhamis, 19 ga watan Disamba a garin Legas.

KU KARANTA: Buhari ya bayyana alhininsa game da rashin dan uwansa Abdullahi Dauda

Hukumar NPA tace jiragen guda 60 suna dauke da kayayyakin abinci da kuma sauran kayan amfani nay au da kullum, kuma ana sa ran zasu sauka ne a tashoshin ruwan Najeriya guda biyu; Tsibirin Tincan da tashar Apapa.

Wasu daga cikin kayayyakin da jiragen suke dauke dasu sun hada da man fetir, iskar gas, sundukai, karafa, siga, daskararren kifi, gishiri, fulawa, motoci da babura, da sauran hajojin yan kasuwa.

Hukumar ta kara da cewa a yanzu haka akwai jiragen dankaro guda 55 da suka iso tashoshin ruwan Najeriya guda biyu suna jiran umarnin fara sauke kaya, haka zalika akwai jirage 36 da a yanzu haka suke sauke kayan da suka dauko.

Daga karshe hukumar ta ce akwai kuma jirage guda 9 su ma dauke da kaya da suka nufo Najeriya, amma kuma sun fasa tafiyar tasu, don haka sun juya inda suka fito.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Zamfara a karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta umarci wani kamfani mai suna Allied-Trading firm, mallakin tsohon gwamnan jahar Kebbi, Sanata Adamu Aliero daya dawo mata da zambar kudi naira biliyan 22 na kwangilar da aka bashi amma bai yi ba.

Tun a shekarar 2013 tsohuwar gwamnatin Abdulaziz Yari ta bayar da kwangilar samar da wutar lantarki a garuruwa da kauyuka 75 na jahar Zamfara ga kamfanin, amma ba ta yi ba duk da an biyata naira biliyan 22.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel