Watan Junairu za'a fara layin dogon Ibadan zuwa Kano - Amaechi

Watan Junairu za'a fara layin dogon Ibadan zuwa Kano - Amaechi

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a jiya ya bayyana cewa da yiwuwan gwamnatin tarayya ta fara ginin layin dogon Ibadan zuwa Kano daga watan Junairu 2020 idan bankin kasar Sin ta bada kudin kwangilan.

Amaechi ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa, Aso Villa, yayinda yake hira da manema labarai bayan taron majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ya kara da cewa za'a cigaba da sufurin mutane daga Legas zuwa Ibadan kyauta har watan Afrilu 2020 da shugaba Buhari zai kaddamar da aikin.

Yace: "Muna sa ran bakin China zata bada bashin ginin layin dogon Ibadan zuwa Kano a Junairu. Idan suka basa, muna sa rana fara aiki a watan Junairu ko Febrairu."

"Hakazalika zamu sa kan jirgin DMU daya da tarago guda biyu ga Ibadan-Legas a watan Juaniru domin daukan mutane kyauta har watan Afrilu da shugaban kasa zai kaddamar."

A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu sabbin jiragen kasa guda biyu da tarago guda 8 wadanda gwamnati za ta daurasu a kan layin dogo daya tashi daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Kaduna.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban kasa zai kaddamar da jiragen ne a watan Janairu, kamar yadda ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya tabbatar ma manema labaru yayin da yake jawabi a fadar gwamnati Aso Rock Villa a ranar Laraba.

KU KARANTA:

Amaechi ya tattauna da manema labarun ne bayan dogon zama da majalisar zartarwa ta gudanar na tsawon sa’o’i 8 a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace gwamnati ta sayo sabbin jiragen ne sakamakon karuwar fasinjoji dake bin jirgin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel