Shugaban kasa ya yi wa wasu manyan Jami’an gwamnati canjin Ma’aikata

Shugaban kasa ya yi wa wasu manyan Jami’an gwamnati canjin Ma’aikata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da canzawa wasu Sakatarorin din-din-din 10 da aka yi wurin aiki, sannan an rantsar da wasu sababbin Sakatarorin na din-din-din har su 9.

Mukaddashiyar shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya ta kasa, HoCSF, Dr. Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana wannan a wata takarda da ta fitar ta bakin Darektar yada labarai na ofishin ta.

A jawabin da Olawunmi Ogunmosunle ta fitar Ranar Laraba, 18 ga Watan Disamban 2019 a garin Abuja, mun ji cewa wadanda aka sakewa wurin aiki sun hada Misis Esther D. Walson-Jack.

An dauke Dr. Abdulkadir Mu’azu daga ma’aikatar ma’adanai zuwa ta harkar gona. Dr. Mohammed Bello Umar ya tashi daga ma’aikatarsa ta harkar gonar zuwa ma’aikatar kimiyya da fasaha.

KU KARANTA: Osinbajo ya na jagorantar zaman NEC na karshen shekara

Sauran wanda abin ya shafa sun hada da: Olusade Adesola ta ma’aikatar Matasa da wasanni, Gabriel Aduda da ke ofishin SGF, sai kuma Bitrus B. Nabasu da ya koma Ma’aikata Neja-Delta.

An dauke Afolabi Ernest Umakhire daga ma’aikatar kasafi zuwa OHCSF. Maurice Nnamdi Mbaeri ta bar hukumar ‘Yan Sanda zuwa ma’aikatar. An canzawa Dr. Bakari Wadinga wurin aiki.

Sababbin Sakatarorin da aka rantsar a kasar su ne: Olusola Olayinka Idowu a ma’aikatar kasafi. An tura Dr. Evelyn N. Ngige, David Adejo Andrew da Nebeolisa Victor Anako OHCSF da PSC.

Sauran wadanda shugaban kasar ya nada sun hada da Aliyu Ahmed, Tijjani Idris Umar, Dr. Nasir Sani- Gwarzo, Temitope Peter Fashedemi da kuma Haasan Musa. Nan gaba duk za su shiga ofis.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel