Daga ranar farko zuwa ranar karshen yadda shirin tsige Trump ya wakana

Daga ranar farko zuwa ranar karshen yadda shirin tsige Trump ya wakana

AFP ta kawo jeringiyar yadda abubuwa su ka wakana har aka kai ga tsige shugaban Amurka Donald Trump a majalisar wakilai. Kafin Trump ya bar ofis, sai Sanatoci sun kada kuri’arsu.

25 ga Yuli

Donald Trump ya yi magana da sabon shugaban kasar Ukraine da aka zaba Volodymyr Zelensky na tsawon mintuna 30 a wayar salula.

Kafin nan Trump ya dakatar da gudumuwar miliyoyin dalolin da Amurka ta saba ba Ukraine.

12 ga Agusta

Wani boyayyen jami’in tsaron kasar Amurka ya fara bankadowa Duniya wayar sirrin da aka yi tsakanin Trump da shugaba Zelensky.

11 ga Satumba

Fadar shugaban kasa ta saki gudumuwar da aka saba ba Ukraine domin magance matsalar tsaro.

24 ga Satumba

Fara binciken Donald Trump da zargin tursasawa Ukraine ta gudanar da bincike a kan Joe Biden wanda ake ganin zai kara da Trump a zabe.

KU KARANTA: Shugabannin da aka tunbuke Amurka da irin laifuffukan da su ka yi

Daga ranar farko zuwa ranar karshen yadda shirin tsige Trump ya wakana

Majalisar Wakilai ta samu Trump da laifi a matsayin shugaban kasa
Source: UGC

25 ga Satumba

An saki rahoton wayar da aka yi tsakanin Trump da Zalensky, inda aka tabbatar Trump ya sa ayi bincike game da Joe Biden da ‘Dansa.

26 ga Satuma

An fito da bayanan sirrin da wani ya saki na zargin Trump da amfani da ofishinsa wajen tasiranta zaben 2020 da kuma kokarin boye wasu bayanai.

Nuwamba 13-21

A wannan lokaci aka fara sauraron jama’a a kwamitocin majalisa. Tsohon Jakadan Ukraine da manyan jami’an Amurka sun bada shaida a majalisa.

3 ga Watan Disamba

An fito da rahoton binciken da aka yi kan zargin Trump da aikata laifuffukan da ake zarginsa da su.

10 ga Disamba

Majalisar wakilai ta fito da laifuffuka biyu da za a kama Donald Trump da su.

18 ga Disamba

An samu Donald Trump da duka laifuffukan da ake tuhumarsa da su a Majalisa. ‘Yan majalisa 230 su ka kada kuri’a cewa shugaban kasar ya yi laifi, 197 su ka nemi ka da a tsigesa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel