Tashin hankali: An kashe ango da duka a lokacin da ake tsaka da shagalin bikinsa

Tashin hankali: An kashe ango da duka a lokacin da ake tsaka da shagalin bikinsa

- Wani ango mai shekaru 30 a California ya hadu da ajalinshi a liyafar bikinshi

- Wasu ‘yan uwa biyu ne suka far ma angon inda suka mishi dukan tsiya, lamarin da ya kawo ajali

- Bayan tsananin buguwar da angon yayi a kanshi, an garzaya dashi asibiti inda ya rigamu gidan gaskiya

Wani mutum mai shekaru 30 a California, ya rasa ranshi a yayin liyafar bikin aurenshi, sa’o’i kadan bayan da aka daura mishi aure da rabin ranshi.

Kamar yadda rahoto ya nuna, wasu ‘yan uwa biyu da ba a gayyata ba ne suka halarci liyafar bikin, kuma suka yi wa angon mugun dukan da yayi ajalinshi.

Ango mai suna Joe Melgoza mai shekaru 30 a duniya, ya rasa ranshi ne wajen liyafar. An hareshi ne a Chino dake California wajen karfe 2:20 na daren ranar Lahadi.

Tashin hankali: An kashe ango da duka a lokacin da ake tsaka da shagalin bikinsa

Tashin hankali: An kashe ango da duka a lokacin da ake tsaka da shagalin bikinsa
Source: Facebook

Angon ya samu muguwar buguwa ne a kanshi inda aka hanzarta garzayawa dashi asibitin Chino Valley Medical Center, inda ya mutu.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan ta'adda sun kwace wani yanki a wata jihar Najeriya har sun kafa tutar su

Jami’an tsaro sun gano wadanda suka hari angon ‘yan uwan juna ne. Rony Aristides Castaneda Ramirez mai shekaru 28 da Josue Daniel Castaneda Ramirez mai shekaru 19 ne suka aikata aika-aikar.

Joe Melgoza ya rasu ya bar matarshi, wacce aka daura musu aure sa’o’i kalilan kafin mutuwarshi tare da ‘yar shi mai shekaru 11.

Kwatanta irin halin da amarya Esther Bustamante Melgoza ta shiga baya kwatantuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel