Da duminsa: 'Yan ta'adda sun kwace wani yanki a wata jihar Najeriya har sun kafa tutar su

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun kwace wani yanki a wata jihar Najeriya har sun kafa tutar su

- Mazauna yankin Orin-Ekiti, na karamar hukumar Ido/Osi sun bazama zanga-zanga tare da neman taimakon gwamnati

- Kamar yadda mazauna yankin suka sanar, ‘yan daba sun sa musu dokar ta baci kuma suna lalata musu amfanin gona

- Sun bayyana yadda ‘yan ta’addan suka kafa tutarsu a yankin, lamarin da ‘yan sanda da gwamnatin jihar suka musanta

Mazauna yankin Orin-Ekiti a karamar hukumar Ido/ Osi na jihar Ekiti a ranar Laraba sun fito zanga-zanga, a kan zargin kutsen da ‘yan ta’adda suka yi musu a wani yankin.

Masu zanga-zangar sun samu jagorancin Bamidele Fasuyi, wanda yace rayukansu na fuskantar barazana sakamakon tutar ‘yan ta’addan dake kafe a yankin. An kara da zargar ‘yan ta’addan da lalata amfanin gonar manoma 70.

A yayin magana da manema labarai, Fasuyi ya zargi ‘yan ta’addan da mamayewa tare da lalata amfanin gonaki da suka fi aka 2500 na gonakinsu.

“Abinda suke son yi shine korar mu daga muhallinmu. Sun kashe daya daga cikin mutanenmu a wannan shekarar,” in ji shi.

“Sun saka mana dokar ta baci a garin. Matasa basu iya zuwa gona kuma gwamnati ta zuba ido tana kallonmu. An lalata hekta masu yawa na gonakinmu. Suna amfani da AK 47 ne cikin dare.”

KU KARANTA: A shirye nake ga duk mutumin da yake bukatar aurena - Rahama Sadau

A lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda yankin, Abutu Sunday ya tabbatar da cewa hukumar bata san da wannan cigaban ba.

“Bamu san da hakan ba saboda babu wanda ya kawo wannan rahoton garemu. Kamar yadda kuka lissafo, zamu fara bincike don gano tushen al’amarin,” in ji shi.

Muyiwa Olumiluaa, kwamishinan yada labarai na jihar, ya ce gwamnati ta san da zanga-zangar da yankin suka yi, amma bata san na kafa tutar ‘yan ta’addar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel