Yanzu-yanzu: Buhari ya shilla jihar Kano

Yanzu-yanzu: Buhari ya shilla jihar Kano

Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja zuwa jihar Kano domin halartan taron yaye daliban kwalejin horon yan sanda dake karamar hukumar Wudil.

An gayyaci Buhari bikin yaye sabbin hafsoshin karo na biyu a matsayin bako na musamman a yau Alhamis, 19 ga Disamba, 2019.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel