Gwamna Yahaya Bello ya ruguza Majalisar Kwamishinonin jihar Kogi

Gwamna Yahaya Bello ya ruguza Majalisar Kwamishinonin jihar Kogi

Mun ji cewa a Ranar Laraba, 18 ga Watan Disamba, 2019, gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ruguza kaf Majalisarsa.

Mai girma gwamnan ya ce wannan mataki da ya dauka a tsakiyar makon nan zai fara aiki ne nan-take ba tare da wata-wata ba.

Gwamnan ya umarci masu rike da mukamai da su mika ragamarsu ga jami’an da su ka fi matsayi a duk ma’aikatar da su ka yi aiki.

Alhaji Yahaya Bello ya godewa wadannan mutane da ya zaba su ka yi wa gwamnatin jihar Kogi aiki a matsayin Kwamishinoni.

Wannan sallama da aka yi ba ta shafi Sakatariyar gwamnatin jihar ba, Folashade Ayoade Arike ta na rike da kujerar ta har yanzu.

Darekta Janar na harkar yada labarai, Kingsley Fanwo, ya zama Mai bada shawara a kan harkar yada labarai da sadarwa na gwamnan.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya ci zaben Gwamnan Kaduna - Inji Kotun koli

Idris Hashiru wanda ya rike Kwamishinan kudi ya koma Mai bada shawara ga gwamna a kan harkar kasafin kudi da tsare-tsaren jihar.

The Nation ta ce Momoh Jibril da Yakubu Okala sun dawo kan kujerunsu na babban Akawun jihar da kuma babban Mai binciken kudi.

Shi ma Mallam Muhammed Onogu ya yi dacen komawa kujerarsa ta babban Sakataren harkokin yada labarai na gwamnatin Yahaya Bello.

Idan ba ku manta ba kwanakin baya gwamnan na APC ya sallami wasu Hadimansa na SA, da SSA bayan ya lashe zaben tazarce a jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel