Buhari ya bayyana alhininsa game da rashin dan uwansa Abdullahi Dauda

Buhari ya bayyana alhininsa game da rashin dan uwansa Abdullahi Dauda

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa tare da jimamin babban rashi da dangisa suka yin a mutuwar Abdullahi Dauda, wani dan yayansa da ya rigamu gidan gaskiya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaba Buhari ya yi addu’an Allah Ya jikan mamacin, Allah Ya gafarta masa sa’annan kuma Allah Ya baiwa iyalansa da sauran danginsu hakurin rashi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai kaddamar da sabbin jiragen kasa masu zuwa Kaduna daga Abuja

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin ne ta hannun tawagar gwamnati daya aika zuwa gidan mamacin dake garin Kaduna a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba.

Buhari ya bayyana mamacin a matsayin mutumin da rayu rayuwar da ta zamto abin koyi ga na baya, kamar yadda shugaban tawagar kuma babban sakataren fadar shugaban kasa, Jalal Arabi ya shaida ma iyalan mamacin.

Tawagar shugaban kasan ta kunshi Sarki Abba, Garba Shehu, Lawal Kazaure, Abdulkarim Dauda, Sabiu Yusuf Tunde, Sha’aban Ibrahim Sharada da Nuhu Sani sun samu tarbar yayyun mamacin, Mamman Daura da Abdulmudallab Daura.

Daga karshe su ma dangin shugaba Buhari sun bayyana godiyarsu da damuwar daya nuna da wannan mutuwa da har ya turo wakilansa zuwa gidan mamacin domin aiko da ta’aziyyarsa garesu.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan siyasar Najeriya, musamman masu burin tsayawa takara ko wacce iri a zaben shekarar 2023 dasu kada su kuskura su sanya shi cikin sabgar siyasarsu.

Buhari ya nemi yan siyasa masu burin tsayawa takara a zaben 2023 da su kasance sun yi aiki tukuru wajen yakin neman zabe, domin kuwa a wannan karo ba zai sake bari a yi amfani da sunansa wajen tafka magudin zabe ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel