Ganduje: Sabbin dokokin masarautu za su fara aiki

Ganduje: Sabbin dokokin masarautu za su fara aiki

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a ranar Laraba, ya yi alkawarin tabbatar da tanadin dokokin sabbin kirkirarrun masarautun jihar guda hudu. Ya ce, sabbin masarautun sun zo zama ne daram.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a taron majalisar zartarwa ta jihar, ya kara da cewa: "Zamu duba dokokin da kyau kuma mu ga bangarorin da ke da bukatar tabbata. Ina tabbatar muku da cewa, zamu tabbatar da duk wasu sassa na dokar, kashi 100, ba tare da wani shinge ba,"

Ganduje ya yi watsi da kiran dattawan jihar Kano wadanda suka samu jagorancin Alhaji Bashir Othman Tofa, na dakatar da kirkirarrun sabbin masarautun, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya ce: "Wadanda suke kiran kansu da dattijan Kanon sunfi samun damar yin abunda zai kawo kalubale ga habakar jihar Kano din baki daya."

DUBA WANNAN: Marin dan majalisa: Majalisar jihar ta bukaci a cafko shugaban karamar hukuma

"Duk na bogi ne! Mutane ne da basu san tarihi ba, gargajiyanci kuma basu goyon bayan sauyi. Kafin nan, akwai hukumar 'yan sanda, kotu da gidan yari duk a karkashin sarautar gargajiya. Amma abinda aka samu yanzu ya biyo bayan sauye-sauye ne. Babu jama'a ko hukumar da take tsaye waje daya. Komai yana sauyawa." cewar gwamnan.

"Duk wadannan sabbin masarautun an kirkirosu ne don habaka jihar ne ta kowanne bangare." in ji sarkin.

Gwamnan ya kalubalanci masu sukarsa a kan "su je sabbin kirkirarrun masarautun su sanarwa mutane cewa, dattijai basu da bukatar masarautar. Ba zasu iya hakan ba".

Nan ba da dadewa ba zasu gane cewa wadannan dattijan basu kaunar cigaban jihar baki daya. Su je suyi ta cewa basu goyon bayan kirkirar sabbin masarautun, cewar Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel