Sanatoci sun tabbatar da Nami a matsayin sabon Shugaban FIRS

Sanatoci sun tabbatar da Nami a matsayin sabon Shugaban FIRS

A halin yanzu, gwamnati ta tabbatar da cewa Muhammad Mamman Nami ya canji Babatunde Fowler a matsayin shugaban hukumar FIRS na kasa.

Kamar yadda mu ka samu labari, Majalisar dattawan kasar ta amince da nadin da aka yi wa Muhammad Nami a hukumar tara haraji watau FIRS.

Sanatocin Najeriya sun tantance Muhammad Nami ne a jiya Ranar Laraba, 18 ga Watan Disamban 2019. Majalisar ta bayyana wannan a zaman da ta yi.

Wannan zama da aka yi jiya, shi ne kusan zaman karshen majalisar a wannan shekara. Ana sa rai ‘Yan majalisar za su tafi dogon hutu zuwa farkon badi.

KU KARANTA: An dura a kan Sanatoci game da batun gyare-gyaren N37b

Sanatoci sun tabbatar da Nami a matsayin sabon Shugaban FIRS

Muhammad Nami ya tsallake matakin Majalisar Dattawa
Source: Twitter

Idan ba ku manta ba a Ranar 9 ga Watan Disamban nan ne fadar shugaban kasa ta aikowa Sanatoci takarda, ta na rokon a tantance sabon shugaban FIRS.

An yi wannan ne kwana guda da cikar wa’adin Mista Babatunde Fowler wanda ya rike wannan kujera na tsawo shekaru hudu, tun daga 2015 zuwa 2019.

A zaman da ‘Yan majalisar su ka yi a jiya, sun amince da Muhammadu Nami. Haka zalika sun sa James Yakwen Ayuba cikin masu lura da hukumar.

Tunde Fowler ya bukaci gwamnatin Buhari ta kara masa wani wa’adin, amma ba a karbi wannan roko na shi ba, har ma an fara jifansa da wasu zargi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel