Shugaba Buhari zai kaddamar da sabbin jiragen kasa masu zuwa Kaduna daga Abuja

Shugaba Buhari zai kaddamar da sabbin jiragen kasa masu zuwa Kaduna daga Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu sabbin jiragen kasa guda biyu da tarago guda 8 wadanda gwamnati za ta daurasu a kan layin dogo daya tashi daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Kaduna.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban kasa zai kaddamar da jiragen ne a watan Janairu, kamar yadda ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya tabbatar ma manema labaru yayin da yake jawabi a fadar gwamnati Aso Rock Villa a ranar Laraba.

KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta soke kwangilolin da Abdulaziz Yari ya bayar na N80bn

Amaechi ya tattauna da manema labarun ne bayan dogon zama da majalisar zartarwa ta gudanar na tsawon sa’o’i 8 a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace gwamnati ta sayo sabbin jiragen ne sakamakon karuwar fasinjoji dake bin jirgin.

Amaechi ya tabbatar da matafiya cewa za’a samu saukin zirga zirga sosai zuwa watan Janairu da zarar an kaddamar da sabbin jiragen da taragonsu, tare da rage wahalhalun da matafiya ke fama da shi, duba da cewa babban titin Kaduna zuwa Abuja na fama da matsalar ayyukan yan bindiga.

“Kamar yadda na fada a baya, taragonmu masu cin fasinjoji 300 ne kawai saboda shi ne abinda masana suka tabbatar mana bayan sun gudanar da bincike, amma a yanzu mun samo mai cin fasinjoji 3,700, muna kara yawan taragon a kullum.” Inji shi.

Haka zalika ministan yace shugaba Buhari zai kaddamar da jirgin kasa daga Itakpe zuwa Warri a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu, haka zalika jirgin Legas zuwa Ibadan zai kammalu kafin watan Afrilu.

Bugu da kari ministan yace kasar China za ta amince da bashin da Najeriya ta nema don aikin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano a watan Janairun 2020, inda yace da zarar kudin sun shigo aiki zai fara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel