Biliyan 37 da aka warewa Majalisar Tarayya ta yi gyara ya na jawo surutu

Biliyan 37 da aka warewa Majalisar Tarayya ta yi gyara ya na jawo surutu

Gwamnatin tarayya ta Majalisar Tarayya ta warewa majalisa kudi har Naira biliyan 37 domin ta yi wasu gyare-gyare. Wannan mataki da aka dauka bai kwantawa ‘Yan Najeriya da-dama ba.

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta soki wannan kudi da za a batar, inda ta ce kashe biliyan 37 wajen gyara ginin da aka yi a kan Naira biliyan 7 ya nuna cewa sata kurum APC ta nufa a fili.

A wani bincike da Jaridar Daily Trust ta yi, ta gano cewa za a iya amfani da wannan kudi wajen yin wasu aikace-aikacen da su ka fi yi wa majalisar kasar kwaskwarimar da zai amfani tsirarru.

Daga cikin abubuwan da Naira biliyan 37 za su iya yi a Najeriya akwai:

1. Gina dakunan karatu 10, 000

Naira biliyan 37 za su isa a gina dakunan karatun makarantun boko fiye da 10, 300 a Najeriya. Wannan zai taimaka wajen inganta harkar ilmi da ya shiga cikin halin ha’ula’i a halin yanzu.

2. Gidajen zama 12, 000

Ma’aikatar gidaje da ayyukan Najeriya za ta iya gina gidaje sama da 12, 300 da wannan makudan kudi. Kowane gida mai dauke da dakuna biyu zai tashi a kan akalla Naira miliyan uku kenan.

KU KARANTA: Sanata ya nemi a binciki zargin tsangwamar 'Yan Najeriya a Ghana

3. Dakunan shan magani 27, 000

Da ace wannan kudi za su shiga hannun ma’aikatar lafiya, za a samu matukar sauyi a harkar kiwon lafiya a kasar nan. Da wannan kudi, za a samu dakunan shan magani akalla 27, 000.

4. Inganta Jami’o’i 37

Akwai jami’ar tarayya akalla guda a kowace jiha da ke Najeriya har da birnin tarayya Abuja. Wadannan kudi za su isa a warewa kowace Jami’a biliyan 1 domin a babbako da harkar ilmi.

5. Taimakawa ‘Yan kasuwa 1, 000, 000

Naira biliyan 37 za ta isa a rabawa kananan ‘yan kasuwa N37, 000 domin su kara jari ko kuma su fara wata karamar sana’ar. Haka zalika za a iya rabawa Manoma wannan kudi su yi aikin gona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel