Gwamnatin Zamfara ta soke kwangilolin da Abdulaziz Yari ya bayar na N80bn

Gwamnatin Zamfara ta soke kwangilolin da Abdulaziz Yari ya bayar na N80bn

Gwamnatin jahar Zamfara a karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta umarci wani kamfani mai suna Allied-Trading firm, mallakin tsohon gwamnan jahar Kebbi, Sanata Adamu Aliero daya dawo mata da zambar kudi naira biliyan 22 na kwangilar da aka bashi amma bai yi ba.

Jaridar Blueprint ta ruwaito tun a shekarar 2013 tsohuwar gwamnatin Abdulaziz Yari ta bayar da kwangilar samar da wutar lantarki a garuruwa da kauyuka 75 na jahar Zamfara ga kamfanin, amma ba ta yi ba duk da an biyata naira biliyan 22.

KU KARANTA: Barawon burodi, madara, kwai da man bota ya fuskanci hukuncin bulala a gaban Alkali

Kwamishinan ayyuka da sufuri na jahar Zamfara, Injinya Isaah Mayana ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 17 ga watan Disamba bayan kammala zaman majalisar zartarwar jahar daya gudana a fadar gwamnati dake Gusau.

Kwamishinan yace gwamnati ta bayar da kwangilar ne a kan kudi naira biliyan 25, amma duk tsawon lokacin da aka dauka aikin da kamfanin ta gudanar bai wuce kashi 60 ba, don haka Gwamna Matawalle ya soke kwangilar.

Haka zalika gwamnatin jahar Zamfara ta soke wasu kwangiloli guda biyu da tsohuwar gwamnatin Yari ta bayar a kan kudi naira biliyan 27 don samar da ruwan famfo a kauyukan jahar wanda ta baiwa kamfanin China Zongo tun a shekarar 2013 amma ya dinga tafiyar hawainiya.

A wani labarin kuma, a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba ne kotun kolin Najeriya ta hannun alkalanta ta yanke wasu hukunce hukunce a kan shari’un dake gabanta game da zaben wasu gwamnonin Najeriya daya gudana a farkon shekarar 2019.

Wadannan gwamnoni sun hada da: Dapo Abiodun na jahar Ogun, Nasir Ahmad El-Rufai na jahar Kaduna, Abdullahi Sule na jahar Nassarawa, Aminu Bello Masari na jahar Katsina, Babajide Sanwo Olu na jahar Legas, Udom Emmanuel Udom na jahar Akwa Ibom, David Umahi na jahar Ebonyi da kuma Seyi Makinde na jahar Oyo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel