Buhari ya na farin ciki da aikin ku – Gbajabiamilla ga ‘Yan Majalisar Wakilai

Buhari ya na farin ciki da aikin ku – Gbajabiamilla ga ‘Yan Majalisar Wakilai

A wani zama da aka yi a makon nan, Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya shaidawa abokan aikinsa cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ji dadin aikin da su ka yi.

A Ranar 18 ga Watan Disamban 2019, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi magana game da martanin shugaban kasa a kan aikin kasafin kudin shekara mai zuwa da aka karkare a kwanan nan.

Gbajabiamila ya ke fadawa Majalisa cewa Mai girma shugaban kasa ya godewa ‘Yan majalisar wakilai da su ka nuna kishin-kasa wajen amincewa da kasafin kudin na 2020 a kan kari.

A Ranar 17 ga Watan Disamban, 2019, ne shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannunsa a kan kasafin kudin shekara mai zuwa. Hakan na zuwa ne bayan 'Yan majalisa sun gama na su aikin.

KU KARANTA: Atiku ya roki Majalisa, ka da ta yarda Buhari ya sake aro $29.9b

Daga cikin aikin da majalisa ta yi shi ne ta kara yawan abin da za a kashe a shekarar badi daga Naira tiriliyan 10.33 zuwa tiriliyan 10.6. Shugaban kasar ya amince da wadannan kwaskwarima.

“Ina so in isar maku da sakon shugaban kasa na godiya ga dukanninku kan aikin da ku ka yi wajen kammala aikin kundin kasafin kudi a wani lokacin da ba a taba yi a tarihi ba.” Inji Kakakin.

Femi Gbajabiamilla ya ce: “Shugaban kasar ya godewa daukacin ‘Yan majalisa a kan jajircewar da su ka yi wajen ganin an dawo da tsarin kashe kudi ya koma daga Junairu zuwa Disamba.”

Bayan ya gama wannan jawabi, Kakakin majalisar ya dauka lokaci ya godewa Takwarorin na sa game da irin yadda su ka yi aiki kawo yanzu, sannan ya yi wa kowa fatan hutun Kirismeti lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel