Amurka: Clinton da Johnson kadai aka tsige kafin Donald Trump a Majalisa

Amurka: Clinton da Johnson kadai aka tsige kafin Donald Trump a Majalisa

Kafin wannan rana ta 19 ga Watan Disamban 2019, majalisar wakilan kasar Amurka ta taba tsige shugabannin kasashe biyu ne rak a tarihi. Yanzu shugaba Donald Trump ya zama na ukunsu.

Duk da majalisar wakilai ta tsige shugabannin, ba su bar ofis ba. A dokar Amurka, sai Sanatoci sun zauna sun kada kuri’a kafin a fatattaki shugabn kasa daga ofis, abin da ba a taba yi ba.

Ga jerin shugabannin da Majalisa ta taba tsigewa a Amurkan:

1. Andrew Johnson

Shugaba Andrew Johnson ya samu kansa a cikin tsaka mai-wuyan siyasa bayan ya gaji Abraham Lincoln. Wannan ya faru ne jim kadan bayan kammala yakin basasan da aka yi a Amurka.

Johnson ya tsige Ministan yakin Amurka, Edwin M. Stanton wanda Mai gidansa Abraham Lincoln ya nada kafin a kashe shi. Johnson ya zargi Stanton da hada-kai da Abokan gaba.

KU KARANTA: Majalisar Amurka ta tsige Shugaba Donald Trump

A dalilin wannan ‘Yan majalisar wakilan tarayya na hamayya su ka dage har su ka tsige shi bisa laifin sabawa dokar wa’adi. A karshe Sanatoci sun zabi ya cigaba da zama a ofis a 1868.

2. Bill Clinton

A shekarar 1998 Majalisar kasar Amurka ta fara bincike a kan shugaban kasa Bill Clinton. An zargi Bill Clinton da kokarin samun alaka da wata Budurwa da ta ke aiki a fadar shugaban kasa.

Wannan Budurwa a lokacin mai suna Monika Lewinsky ce ta jefa shugaba Bill Clinton cikin matsala. An samu Clinton da laifin yi wa kuliya karya bayan ya kama kansa da kansa a bincike.

Majalisar wakilai ta tsige bisa zargin samun sa da laifin karya da kuma kokarin shiga-gaban shari’a. A farkon 1999 Sanatoci su ka zabi Clinton ya cigaba da zama a ofis bayan sun kada kuri’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel