Zaben 2019: Jerin gwamnoni 8 da kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasararsu

Zaben 2019: Jerin gwamnoni 8 da kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasararsu

A ranar Laraba, 18 ga watan Disamba ne kotun kolin Najeriya ta hannun alkalanta ta yanke wasu hukunce hukunce a kan shari’un dake gabanta game da zaben wasu gwamnonin Najeriya daya gudana a farkon shekarar 2019.

Sai dai dayawa daga cikin gwamnonin da kararsu ta kai har gaban kotun koli sun sha, sakamakon kotun ta tabbatar da halascinsu a matsayin gwamnoni tare da yin fatali da korafe korafen abokan hamayyarsu da suka gabatar mata.

KU KARANTA: Da zafi zafi: Wani babban Sanatan jam'iyyar APC daga kudancin Najeriya ya rasu

Wadannan gwamnoni sun hada da: Dapo Abiodun na jahar Ogun, Nasir Ahmad El-Rufai na jahar Kaduna, Abdullahi Sule na jahar Nassarawa, Aminu Bello Masari na jahar Katsina, Babajide Sanwo Olu na jahar Legas.

Sauran sun hada da Udom Emmanuel Udom na jahar Akwa Ibom, David Umahi na jahar Ebonyi da kuma Seyi Makinde na jahar Oyo.

Idan za’a tuna, Isah Ashiru Kudan shi ne dan takarar gwamnan jahar Kaduna a karkashin inuwar lemar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 daya gudana a watan Feburairu, sai dai El-Rufai ya lashe zaben da bambamcin kuri’u fiye da dubu dari biyu.

Sai dai Isah Ashiru bai gamsu da sakamakon zaben ba inda ya garzaya gaban kotun sauraron koke koken zabe, inda Alkalan kotun bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu tare da gudanar da dogon nazari suka sanar da El-Rufai a matsayin halastaccen gwamnan jahar Kaduna.

Wannan hukunci bai yi ma Isah Ashiru dadi ba, kai tsaye ya zarce kotun daukaka kara, a nan ma bai ji da dadi ba sakamakon kotun ta yi fatali da kararsa, ta sake tabbatar da nasarar Malam Nasir El-Rufai a matsayin halastaccen gwamnan Kaduna.

Duk da haka Isah Ashiru bai dandara ba, sai ya zarce kotun koli, kotun Allah Ya isa da nufin kwatar hakkinsa tare da bukatar kotun ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara, amma kash! Alkalin kotun koli sun yi watsi da bukatunsa duka saboda rashin gamsassun hujjoji, don haka suka sake tabbatar da halaccin gwamnatin El-Rufai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel