Yanzu-yanzu: Majalisa ta tsige shugaban kasar Amurka

Yanzu-yanzu: Majalisa ta tsige shugaban kasar Amurka

- Majalisar kasar Amurka ta tsige shugaban kasa Donald J. Trump

- A halin yanzu, Trump shine shugaban kasa na uku da aka taba tsigewa a kasar Amurka

- An zargi shugaban kasar da amfani da ofishinsa wajen sa wata gwamnati harar kishiyarsa ta siyasa

Majalisar kasar Amurka ta tsige shugaban kasa Donald Trump daga kujerar mulkin kasar Amurka. ‘Yan majalisar wakilan kasar sun kada kuri’u 230 na goyon bayan tsige shugaban kasar, inda aka samu kuri’u 197 da basu yadda da hakan ba. Wadannan kuri’un kuwa na takardar farko ce da ke zargin Trump da amfani da ikonsa ba ta yadda ya dace ba.

A takarda ta biyu, wacce majalisar ke zarginsa da hanata bincike, an samu kuri’u 229 da ke goyon bayan tsigesa inda 198 basa goyon baya.

DUBA WANNAN: Rikin fili: Yan daba sun yi wa basarake mugun duka, sun bar shi rai hannun Allah

Da wannan ne Trump ya zama shugaban kasa na uku da aka taba tsigewa a tarihin kasar Amurka. An tsigesa ne bayan da aka zargi shugaban kasar da yin amfani da kujerarsa wajen tirsasa wata gwamnatin ketare don harar kishiyarsa ta siyasa.

An zargi Trump da tirsasa kasar Ukraine wajen bude babin bincike a kan kishiyarsa na siyasa, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar, Joe Biden. Ya kara da hana majalisar bincike kuma a kan hakan.

Duk da cewa an tsige shugaban kasar Amurkar, har yanzu yana kan kujerarsa har zuwa lokacin da majalisar dattawan kasar zata amince da hakan.

Wadannan zargin game da Trump sun samu jagoranci ne daga kakakin majalisar wakilan kasar, Nancy Pelosi. A yayin tattaunawa akan tsige shugaban kasar, Pelosi ta ce, basu da wani zabi da ya wuce tsige shugaban kasa trump.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel