Yanzu-yanzu: Majalisar kasar Amurka ta tsige shugaba Donald Trump

Yanzu-yanzu: Majalisar kasar Amurka ta tsige shugaba Donald Trump

- Wasu rahotanni da muke samu sun nuna cewa, a jiya Laraba ne aka tsige shugaban kasar Amurka Donald Trump

- An tsige shine bayan kama shi da laifin hada baki da kasar Ukraine akan tayi kutse akan harkar zaben kasar da za'ayi a shekarar 2020

- Trump dai ya zama shugaban kasa na uku a tarihin shugabancin kasar da aka taba tsigewa

A jiya Laraba ne aka kada kuri'ar tsige shugaban kasar Amurka Donald Trump, inda a karshe wadanda suka nemi a tsige shi suka fi yawa.

An tsige shugaba Donald Trump ne bayan 'yan majalisar kasar sun jefa kuri'u akan tsige shi kamar dai yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

A cikin 'yan majalisa 435 da suka jefa kuri'a a akan wannan zabe da aka gabatar, 'yan majalisu 230 sun nemi a tsige shugaban kasar, inda 197 kuma suka nemi a barshi ya cigaba da mulki.

Hakan ne ya mayar da shugaban kasar na 45 damar zama shugaban kasa na uku da aka taba cirewa a kundin tarihin kasar ta Amurka.

KU KARANTA: Mijina yayi min saki uku saboda na bukaci kwanciya da abokinshi - Mata

Kasar ta Amurka tana zargin shugaba Donald Trump da hada kai da kasar Ukraine akan ta gabatar da bincike akan abokin takarar shi na jam'iyyar Democrats, Joe Biden akan zaben da za ayi na kasar a shekarar 2020.

Wannan dalilin ne ya sanya 'yan kasar ta Amurka zanga-zanga akan sai a tsige shugaban kasar, tunda har ya hada baki da wata kasa akan tayi kutse akan lamuran zaben kasar.

Ganin cewa hakan ba karamin zubarwa da kasar mutunci zai yi ba a idon duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel